Jamus na son a tallafawa ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 26.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus na son a tallafawa 'yan gudun hijira

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci hadin kan al'ummar kasar wajen tallafawa 'yan gudun hijirar da kasar ta karba a 'yan kwanakin da suka gabata.

Merkel din ta yi wadannan kalamai ne lokacin cikin jawabi da ta saba yi mako-mako wanda a wannan karon ya zo kwanaki kalilan kafin bikin tunawa da ranar hadewar Jamus ta gabas da ta yamma shekaru 25 da suka gabata.

Shugabar ta gwamnatin Jamus ta ce yana da kyau al'ummar kasar su rungumi 'yan gudun hijirar da nufin tallafa musu wajen daidaituwa lamuransu a Jamus din.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da dubban 'yan gudun hijira ke cigaba da kwarara kasashen nahiyar Tturai a wani matki na inganta rayuwarsu wanda kuma galibinsu kan kasance sun shigo nan Jamus ne.