1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na maraba da manufar EU kan Afirka

Ahmed Salisu
December 9, 2019

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya yi maraba da irin alkiblar da kantoman harkokin wajen Kungiyar EU Josep Borrell zai fuskanta kan huldar kungiyar da Afirka.

https://p.dw.com/p/3UUXc
Deutschland 28. Jahrestagung der Deutsch-Polnischen Gesellschaft Bundesverband in Homburg | Heiko Maas
Hoto: Imago Images/photothek/F. Gaertner

Maas ya ambata hakan ne a birnin Brussel na kasar Beljiyam, inda ministocin harkokin waje na kasashen da ke cikin kungiyar ta EU ke wani don tattaunawa kan batutuwa da dama ciki kuwa har da huldar kungiyar da Afirka, inda ya ce Afirka na da muhimmanci gaske ga kungiyar don haka dole ne a sakata a sahun gaba kan irin abubuwan da EU din za ta mayar da hankali a kai.

Minista Maas ya ce ''dole ne EU ta sanya Afirka cikin abubuwa da ke da muhimmanci gareta. Akwai dalilai da dama na yin hakan wadanda suka hada batun 'yan cirani da kuma harkoki na tsaro musamman ma idan aka duba irin abin da ke faruwa a yankin Sahel da kuma kasar Libiya. Don haka ya yi daidai da Josep Borrell ya sanya Afirka a sahun gaba.''