1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da kisan kare dangi ga Yahudawa

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 22, 2020

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya sha alwashin ci gaba da tunawa da ta'addancin da gwamnatin kama karya ta 'yan Nazi ta aikata.

https://p.dw.com/p/3WfBH
Frank-Walter Steinmeier ASEM Asien Europa Treffen Luxemburg
Shugaban kasar Jamus Frank-Walter SteinmeierHoto: picture-alliance/dpa/J. Warnand

Frank-Walter Steinmeier ya bayyana hakan ne a birnin Kudus na Isra'ila, yayin da yake ganawa da Yahudawan da suka tsira daga kisan kare dangin da gwamnatin Nazin ta Jamus ta yi a kansu, yana mai cewa tunawa da wannan aika-aika ya zama wajibi. Steinmeier zai kasance shugaban kasar Jamus mai ci na farko da zai yi jawabi a wajen bikin Holocaust din da zai gudana a wannan Alhamis din, a cibiyar tunawa da ta'asar ta 'yan Nazi ta Yad Vashem da ke Isra'ila. An dai shirya ziyarar musamman ta Steinmeiere ne, domin tunawa da ranar da sojojintsohuwar Tarayyar Soviet suka ceto wadanda aka tsare a sansanin gwale-gwale na Auschwitz na 'yan Nazin, tare da rufe shi a ranar 27 ga watan Janairun, 1945.