Nazi suna ne na masu kyamar baki da nuna wariyar launin fata gami da kyamar Yahudawa. Adolf Hitler da ya mulki Jamus daga 1933 zuwa 1945 shi ne jagoran 'yan Nazi.
Dabi'ar 'yan Nazi ta kyamar baki da Yahudawa ce ta yi sanadin kisan kare dangin da aka yi wa miliyoyin Yahudawa. Bayan kifar da gwamnatin 'yan Nazi a Jamus da ma sauran bangarorin duniya an haramta yadawa da nuna akida irin ta Nazi musamman batu na kyamar Bani Yahudu.