1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu na zargin dattijo da taimakon Nazi

Abdul-raheem Hassan
October 7, 2021

An gurfanar da wani tsoho mai shekara 100 a gaban kotu a kasar Jamus, kan zargin taimakawa sojojin Nazi aikata kisan kai a sansanin tattara bayanai na Sachsenhausen a lokacin yakin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/41P9b
Konzentrationslager Sachsenhausen
Hoto: Getty Images/Newsmakers/Courtesy of the National Archives

Mutumin da ake zargi mai suna Josef S. yana fuskantar laifuka 3,518 na kisan kai tsakanin 1942 zuwa 1945 a lokacin da ya yi aiki a matsayin memba na Jam'iyyar Nazi reshen sojojinta.

Lauyan wanda ake zargi, ​​ya shaidawa kotun wanda ake tuhuma ba ya son yin tsokaci kan zargin da ake masa, amma mahukunta sun ce dattijon ya isa ya tsaya gaban shari'a duk da yawan shekarun mutumin.