1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dage gabatar da manufifin tsaron Jamus

Matthias von Hein ATB/LMJ
May 26, 2023

Tsawon watanni ana jiran bayanan da gwamnatin Jamus za ta fitar kan manufofinta na tsaro. Sai dai kuma an sake dage fitar da bayanan. Abin da ya janyo cece-kuce a cikin gwamnatin.

https://p.dw.com/p/4RsVv
Jamus |  Shugaban Gwamnati | Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Tun cikin watan Janairu ne dai ake ta tsammanin gabatar da kundin bayanan kan tsaron kasa, s sai dai a yanzu ana kyautata zaton majalisar gudanarwa za ta bayar da sahalewa a tsakiyar watan Yuni mai zuwa. Ita ma dai majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, ta dage muhawarar da ta shirya kan daftarin tsaro a ranar 25 ga watan Mayu, daya daga cikin dalilan shi ne tattaunawar da za a yi a Berlin a ranar 20 ga watan Yuni tsakanin gwamnatocin Jamus da Chaina. Batun da ba ya cikin daftarin, kasancewar an jima da tsara shi kuma magana ce ta tsaron kasa kamar sauran batutuwa da suka shafi kasa.

Karin Bayani: Kara karfi ga rundunar sojojin Jamus

An dai kambama batun sabuwar manufar tsaron, inda a karon farko Jamus ke son aiwatar da cikakken nazari kan manufofin harkokin waje da na tsaro a karkashin kammalallen tsarin tsaro. Dangane da wannan tafarki manufar tsaron ta fi gaban batun sojoji da diflomasiyya, a cewar wani dan majalisar dokokin Bundestag na Jam'iyyar SPD Johannes Arlt. A cewarsa akwai abubuwa da dama da za su iya shiga batun manufifin tsaron, kama daga  na Ilimi da lafiya da muhalli da abinci da manufofin harkokin kudi. Kawancen gwamnati mai ci ta SPD da Green da kuma FDP, tuni suka bayyana aniyar samar da manufar tsaro ga fannoni da dama a cikin kawancen gwamnatin.

Jamus | Tsaro | Annalena Baerbock
Ministar harkokin kasashen waje ta Jamus Annalena BaerbockHoto: Kira Hofmann/photothek/picture alliance

Sai dai a wancan lokaci ana zaman lafiya a Turai, a lokacin da aka kaddamar da shata dabarun manufofin tsaron a hukumance tare da jawabin daga ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock a tsakiyar watan Maris na 2022 makonni uku da fara yakin Ukraine. Baerbock ta bayyana lamarin tsaron da tabbatar da kariyar 'yancin rayuwarmu a matsayin ginshikin daftarin, kariya da juriya da kuma dorewa. Su ma dai yan adawa suna iya bayar da goyon bayansu ga wannan kudiri, ga misali dan jam'iyyar CSU a majalisar dokoki Thomas Erndl yana cikin wadanda suka fara dabbaka wannan yunkuri na sabuwar manufa kan tsaro.

Karin Bayani: Bikin tunawa da nasara a kan sojojin NAZI

Erndl ya soki lamirin yawan dage gabatar da kundin manufofin kan tsaro, yana mai cewa ko da yake lallai akwai bukatar samun sakamako mai nagarta amma abin takaici har yanzu ba a ga hakan ba. Tsawon lokaci an danne shirin kafa majalisar tsaron kasa, wanda ba don haka ba ita ce za ta rika tsarawa da tattara bayanai tsakanin sassa dabam-dabam tare da lalubo amsa ga matsaloli da kalubalen da ka iya tasowa, sai dai rashin jituwa kan a ina za a kafa wannan majalisar tsaron kasa ta hana cimma matsaya. Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa ofishin shugaban gwamnati Olaf Scholz da ofishin ministar harkokin waje, kowannensu na so majalisar tsaron ta kasance karkashin ikonsa.