Jamus da Faransa sun taka rawar gani kan batun Girka | Labarai | DW | 13.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da Faransa sun taka rawar gani kan batun Girka

Ministocin harkokin wajan Faransa da Jamus sun ce irin huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta taka rawar gani wajan cimma yarjejeniya kan batun kasar Girka.

Frank-Walter Steinmeier da Laurent Fabius

Frank-Walter Steinmeier da Laurent Fabius

Da ya ke magana a daura da taron tattaunawa kan nukiliyar kasar Iran a birnin Vienna, shugaban diflomasiyyar kasar Faransa Laurent Fabius ya ce, ya na mai tabbatar da cewa irin karfin huldar da ke tsakanin kasashen na Jamus da Faransa ce ta taimaka wajan kaiwa ga wannan matsayi, tare kuma da hada kan dukannin kasashen na Turai.

Shi ma daga nashi bengare Ministan harkokin wajan kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya jaddada cewa, idan da babu kyaukyawar hulda tsakanin kasashen na Faransa da Jamus, da ba'a kai ga cimma wannan yarjejeniya kan kasar ta Girka ba. Kasashen na Turai dai sun amince da wata yarjejeniyar da zata bada damar sake wata tattaunawa don samar wa kasar ta Girka mafita a cikin wani tsari na tallafawa wannan kasa karo na uku bayan da aka shafe tsawon watanni shidda ana wannan tattaunawa.