Jamus ba za ta sayarwa Saudiyya makamai ba | Labarai | DW | 18.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ba za ta sayarwa Saudiyya makamai ba

Gwamnatin Jamus ta tsawaita dokar dakatar da sayarwa Saudiyya makamai nan da watanni shida masu zuwa.

Deutschland Hafen von Mukran | Küstenschutzboot für Saudi-Arabien (picture-alliance/dpa/S. Sauer)

Jamus ta dakatar da sayarawa Saudiyya makamai

Tsawaita matakin na nufin babu yarjejeniyar sayar da makamai ga Saudiyya da gwamnatin Jamus za ta amince da ita har nan da ranar 31 ga watan Maris na shekara ta 2020 mai zuwa. Haka kuma mahukuntan na Jamus sun nunar da cewa hanin ya shafi makaman da aka riga aka amince da sayarwa Saudiyyan, a dangane da haka ba za a mika su ga mahukuntan Riyadh din ba. Tun dai cikin shekara ta 2017 ne gwamnatin Jamus din ta fara sanya dokar hana sayarwa da makaman da Saudiyyan ke amfani da su a yakin da take jagoranta a kasar Yemen, kafin daga bisani mahukuntan na Berlin su dakatar da sayar da makaman baki daya ga Saudiyyan cikin watan Nuwambar shekara ta 2018 da ta gabata, sakamakon kisan da aka yi wa fitaccen dan jaridar nan dan asalin kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi a birnin Santanbul na Turkiyya. Kisan da aka yi shi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan na Turkiyya da kuma ake zargin wasu jiga-jigan masarautar Riyadh da hannu cikinsa.