Jam′iyyar PDP ta yi watsi da zaben da aka yi a Kano | BATUTUWA | DW | 24.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Jam'iyyar PDP ta yi watsi da zaben da aka yi a Kano

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta koka kan yadda zaben gwamna da aka karasa a jiya a Kano ya gudana inda ta zargi jam'iyyar APC da ke mulki a jihar da amfani da 'yan bangar siyasa.

Jam'iyyar ta PDP a Najeriya ta koka saboda abin da ta kira  amfani da 'yan banga da ta zargi APC mai mulki da yi, wajen hana jama'a  zabar abin da suke so, don haka ta ce ba ta dauki zaben a jiya Asabar a matsayin zaben da ba sahihi ba. 

A wata zantawa da ya yi da manema labarai a jiya, shugaban jam'iyyar ta PDP a Kano Rabiu Suleiman Bichi ya ce irin yada aka girke mutane dauke da makamaki da ma yadda suka rika cin zarafin masu kada kuri'a a sassan jihar daban-daban abu da ya sabawa tsarin demokradiyya.

PDP din ta ce a mafi akasarin yankunan da aka gudanr da zaben a jiya, 'yan bangar sun yi ta cin mutuncin mutane saboda cimma burinsu na bata tsarin baki daya.

To sai dai jam'iyyar APC mai mulki a jihar ta musanta kalaman na PDP kan zaben na Kano.