Jamhuriyar Nijar ta fadada yaki da Boko Haram | Siyasa | DW | 08.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamhuriyar Nijar ta fadada yaki da Boko Haram

'Yan Jamhuriyar Nijar sun fara mayar da martani kan matakin kasar na neman taimakon kasar Chadi a yaki da Boko Haram.

Rahotanni daga kasar Chadi na cewa sojojin kasar kimanin dubu biyu dauke da manyan makaman yaki sun kama hanyar zuwa kan iyakar makobciyar kasar Nijar domin taimaka wa sojojin kasar a sabon harin da suka kaddamar kan Kungiyar Boko Haram biyo bayan kazamin harin karshen makon da ya gabata a garin Bosso na kasar ta Jamhuriyar Nijar da ke kan iyaka da Najeriya inda suka hallaka sojojin Nijar 26 da na Najeriya guda biyu.Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa wata majiyar daga sojojin kasar ta Chadi da ba ta bukaci a sakaya sunanta ce ta kwarmata wannan labari da ta ce an bai wa sojojin Chadin umarnin fatatakar mayakan Kungiyar ta Boko Haram. Tun farko Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar ta Nijar ya bukaci takwaransa na Idriss Deby bisa tura sojojin.

A shekara ta 2015 dai rundunar sojojin kasar ta Chadi ta kai irin wannan dauki a kasashen Kamaru da Najeriya dama a Jamhuriyar Nijar a kokarin kasashen na murkushe kungiyar ta Boko Haram.Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu rahotanni daga Jamhuriyar ta Nijar ke cewa sojin kasa masu samun rakiyar jiragen yakin kasar ta Jamhuriyar Nijar sun shiga yanzu haka farautar mayakan Boko Haram a yankin na Bosso.

Sauti da bidiyo akan labarin