Isra´ila ta kai hari a Gaza | Labarai | DW | 27.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta kai hari a Gaza

Wannan shine hari na farko mafi muni, da dakarun bani yahudu su ka abkawa Gaza, tun bayan da ƙungiyar Hamas ta mamaye wannan ziri.

A cewar opishin ministan tsaron Isra´ila, wannan hari na matsayin martani, ga rokokin da wasu yan takifen Hamas su ka cillawa Isra´ila.

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas ya Allah wadai da wannan hari, wanda a cewar sa zai kara maida hannu agogon baya, a yunƙurin cimma zaman lahia, tsakanin Isra´ila da Palestinu.

A ɓangaren diplomatia shugaban hukumar Palestinawa na ci gaba da samun goyan baya, a dangane da tawayen ƙungiyar Hamas.

A ɗaya wajen kuma, Mahamud Abbas ya tsige shugaban rundunar tsaron fadar sa, wanda ya tuhuma da rashin sanin makamar aiki, a sakamakon kashin da dakarun sa su ka sha, daga ƙungiyar Hamas a zirin Gaza.