Iran ta koma aikin inganta sinadaren uraniyum | Labarai | DW | 13.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta koma aikin inganta sinadaren uraniyum

Jamian diplomasiya sun bada rahoto a yau cewa kasar Iran ta fara aikin sarrafa sinadaren uranium a tasharta ta nukiliya na Natanz,wanda ake ganin wani mataki ne farko,na samarda makamashi ko kuma kera makaman atom.

Kasasen yammacin duniya dai suna ganin cewa Iran tana kokarin kera makaman kare dangi ne,sai dai jamian diplomasiya da kwararru akan nukiliya sunce zai dauki Iran kusan shekaru 2 zuwa 10 kafin ta samu fasahar kera makaman idan har tana da niyyar yin hakan.

A gobe talata idan Allah ya kai mu supetocin Majalisar Dinkin Duniya zasu tafi yanin Natanz domin fara duba aiyuka da Iran ta fara.