Hukumomin Jamus da Italiya sun karfafa yaki da ´yan Mafia | Labarai | DW | 01.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Jamus da Italiya sun karfafa yaki da ´yan Mafia

Kasashen Jamus da Italiya sun kuduri aniyar karfafa hadin kai a yaki da kungiyoyi irin na ´yan Mafia. Shugaban hukumar ´yan sandan ciki na Jamus Jörg Ziercke ya fadawa mujallar kasar ta Focus cewa kasashen biyu sun amince da kafa wani sashe na bai daya wanda aikinsa zai kasance gudanar da bincike akan dangantaka tsakanin tsatson Italiyawa da kuma ´yan´uwansu dake nan Jamus. Mista Ziercke ya ce ta haka yana fata za´a samu sabbin bayanai dangane da masu tilastawa mutane a tarayyar Jamus biyan diyya don a kare lafiyar su. Dalilin karfafa wannan hadin kai tsakanin hukumomin guda biyu shi ne kisan gillan da aka yiwa wasu ´yan Italiya 6 a wajen wani gidan abinci a birnin Duisburg kimanin makonni biyu da suka wuce.