Hukumar zabe a Najeriya ta shirya tsab dan zaben gwamnoni | Siyasa | DW | 10.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukumar zabe a Najeriya ta shirya tsab dan zaben gwamnoni

Hukumar zaben kasar ta INEC ta ce ta yi gyara da nufin tabbatar da ingantaccen zaben da babu irinsa a tarihi na kasar.

Yan takara akalla 760 ne dai zasu fafata da nufin cika gurbi na gwamnonin jihohi 29 cikin 36 a bangare daya kuma mutane 5690 za su nemi zama 'yan majalisu na jihohi a cikin zaben dake zaman matakin karshe na tabbatar da tasirin jam'iyyun kasar dama tsari na siyasarta.

Ba dai za'a gudanar da zabukan ba a jihohin Bayelsa da Edo da Anambra da Ondo da Ekiti da Osun da kuma Jihar Kogi sakamkon ragowar wa'adin mulkin gwamnonin jihohin Bakwai.

Duk da cewar dai ta yi nasara cire tutar gudanar da ingantaccen zabe a kusan daukacin sassan sabon zaben dai na zaman zakaran gwajin dafi ga hukumar zaben kasar ta INEC da a baya ta fuskanci jeri na kura kurai kama daga rashin fara zaben a lokaci, ya zuwa gazawar aikin na'urar tantance 'yan zaben a mazabu daban daban.

Alal misali dai sai kusan tsakar rana ne aka fara aikin tantance masu zaben maimakon karfe takwas na safe agogon kasar ta Najeriya, sakamakon gaza isar kayan zabe dama turawarsa zuwa rumfuna abisa na lokaci.

To sai dai kuma a wannan karo a fadar kakakin hukumar zaben na kasa Nick Dazang, hukumar tai nazari ta kuma dauki matakai da nufin tabbatar da ingantaccen zaben da ya darma na shugaban kasar makonni biyun da suka gabata.

"Wannan tangarda ta taso ne sakamakon rashin fahimtarmu da kungiyar ma'aikatan sufuri, mun kuma koma mun sake zama da su muna jin ba za'a sake samun matsalar ba. Zancen na'urar tantancewa mun sake yi wa jami'anmu horo kan amfani da ita. Sannan muna da jami'an ko ta kwana domin warware duk wata mishkila daga na'urar”.

Ko bayan matsalolin rashin isar kayan zaben dama gaza aikin nau'rorin dai akwai kuma matsaloli daga jami'an zaben da aka rika zarga sun hada kai da 'yan siyasa da nufin murde zaben a jihohi daban daban dake kasar.

Can a jihohin Rivers da Akwa Ibom dai alal misali an yi ta zanga zangar kin jini na kwamishinonin zabe na jihar bisa zargin hada baki da nufin agaza wa masu siyasar yankin.

To sai dai kuma kan wannan ma hukumar zaben kasar tace ta gyara da nufin tabbatar da adalci kan kowa a fadar Dazang din.

“Ita hukumar zabe yanzu abun da ta yi shi ne ta tura hukumomi na tarraya domin suje Jihar ta Rivers su tabbatar d adalci kan kowa”

Ana dai kallon sabon zaben gwaji na zahiri a bisa karfin jam'iyyun kasar biyu a tsakanin APC da ke shirin jiran gado da kuma PDP mai tafiya hutu a matakin tarraya.

To sai dai samun nasarar zaben na iya kawo babban sauyi a bisa suna dama kimar kasar ta Najeriya dake takama da jan gaba a nahiyar Africa amma kuma ke fuskantar kalubale na rashin karbabben zabe a lokaci mai nisa

Sauti da bidiyo akan labarin