Hukumar makamashin nukiliya ta fara taron gaggawa akan Iran | Labarai | DW | 02.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar makamashin nukiliya ta fara taron gaggawa akan Iran

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta fara gudanar da wani taron gaggawa na kwana biyu wanda a lokacinsa zata tattauna yuwuwar mika kasar Iran gaban kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya akan shirinta na nukiliya.

A makonnnanne dai wakilan dindindin guda biyar na kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya suka amince da shawarar kira ga kwamitin gudawarwa mai wakilai 35 na hukumar makamashin nukiliyar ta duniya da ya kai Iran din gaban kwamitin .tsaron,abinda yasa babban mai shiga tsakani akan dambarwar nukiliyar na Iran Ali Larijani yace muddin akayi hakan to kuwa Iran zata koma kain dana in kan shirin nata na inganta sinadarin uranium kuma bugu da kari zata kawo karshen duk wata tattaunawa da hadin,kai da take baiwa masu bincike na majalisar dinkin duniya.