Hukumar FAO ta ce kusan yara miliyan 6 ne ke mutuwa a ko wace shekara saboda yunwa. | Labarai | DW | 23.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar FAO ta ce kusan yara miliyan 6 ne ke mutuwa a ko wace shekara saboda yunwa.

Hukumar noma da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, wato FAO a takaice, ta ce yunwa da rashin isashen abinci mai gina jiki na janyo mutuwar yara kusan miliyan 6 a ko wace shekara. A cikin rahotonta na shekara-shekara da ta buga, hukumar ta ce, ko kadan duniya ba ta kusanci cim ma burin nan na rage yunwa a doron kasa zuwa rabin adadinsa, kafin shekara ta 2015 ba.

Mafi yawan wadanda ke fama da wannan illlar ta yunwa kuma, sun fito ne daga Asiya da kuma yankin Afirka bakar fata.