Hukumar binciken gaskiya da afuwa a Liberia ta fara aiki | Labarai | DW | 10.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar binciken gaskiya da afuwa a Liberia ta fara aiki

Hukumar binciken gaskiya, da yin afuwa a kan kissan ƙare dangin, da ya wakana, a ƙasar Liberia, ta fara sauraran ƙarraki, a talatar yau.

Wannan hukuma, za ta saurari shaidu, daga mutanen da haɗarin ya rutsa da su, a tsawan yaƙin da ya ɗaiɗaita ƙasa, Liberia daga 1979 zuwa 2003.

Shugaban wannan hukuma, Jerome Verdier, ya yi kira ga dukkan mutanen da abun ya shafa, su yi ƙoƙarin kawo cikkakun shadu, domin tantance gaskiyar abun da ya wakana, da zumar ɗaukar matakan gyaran gaba.

Hukumar kulla da ci gaba ta Majalisar Ɗinkin Dunia, da ƙungiyoyin tallafi na ƙasashe da dama, su ka saka kuɗaɗen gudanar da wannan aiki, da zai ɗauki tsawan shekaru 2.