HRW ta yi tsokaci a game da sakamakon zaɓe a Nigeria | Labarai | DW | 25.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

HRW ta yi tsokaci a game da sakamakon zaɓe a Nigeria

Hukumar kare haƙƙoƙin bani adama ta ƙasa da ƙasa, wato Human Right Watch, ta bayyana rahoto, a game da zaɓɓuɓukan da su ka wakana a Taraya Nigeria.

Rahoton ya ce, gwamnatin Nigeria, tare da haɗin kan hukumar zaɓe ta INEC, sun tabka maguɗi na ƙin ƙarawa, a zaɓen shugaban ƙasa, na ranar asabar da tawuce.

Shugaban hukumar Human Right Watch, mai kula da nahiyar Afrika, Peter Takirambudde, ya ce maimakon gwamnati, da hukukamr zaɓe, su ba jama´ar ƙasa damar sauke yancin su, na zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana, sai su ka tanadi matakan maguɗi da hargitsi, da zumar cimma burin su, na hauda ɗan takara PDP a kan karagar mulki.

Hukumar kare yancin Bil Adama ta Human Rigth watch ta bayyana yin tur da Allah wadai, da wannann zaɓe.