1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hisbollah ta halaka Isra´ilawa akalla 7 a arewacin Isra´ila

August 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bunu

Akalla mutane 7 sun rigamu gidan gaskiya a wasu hare haren rokoki da Hisbollah ta kai akan arewacin Isra´ila. Wannan dai shi ne adadi mafi yawa na mutanen da aka kashe a lokaci daya a Isra´ila tun bayan fara fadan sama da makonni 3 da suka wuce. Kamar yadda ´yan sanda suka nunar a cikin mintoci kalilan Hisbollah ta harba rokoki akalla 100 akan yankin na arewacin Isra´ila. A kuma wata fafatawa da aka yi ta kasa rudunar sojin Isra´ila ta ce ta rasa sojoji guda 3. Tashar radiyon sojin Bani Yahudu ta ce dakarun sun kutsa zuwa wani yanki mai tazarar kilomita 4 cikin Lebanon. Manufar wannan kutse dai kamar yadda tashar ta nunar shi ne kafa wani yankin da babu yaki a ciki a kudancin Lebanon. Su kuma jiragen saman yakin Isra´ila sun kai hare hare akan wurare sama da 120 a Lebanon, ciki har da wani sansanin ´yan Hisbollah dake kudancin Lebanon din. A kuma can birnin Beirut Isra´ila ta rarraba kasidu inda ta yi kira ga fararen hula a kusa da filin jirgin saman birnin da su gaggauta tashi daga yankin, domin rundunar saman Isra´ila zata tsananta farmakin da take kaiwa yankin.