Harin bama-bamai a yankin arewacin Kamaru | Labarai | DW | 22.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bama-bamai a yankin arewacin Kamaru

Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da mutuwar kimanin mutane 20 sakamakon harin 'yan kunar bakin wake biyu a Maroua da ke arewacin kasar.

Kimanin mutane 20 sun hallaka lokacin da 'yan kunar bakin wake biyu suka tayar da bama-bamai cikin wata kasuwa da ake hada-hada mai shake da jama'a, a garin Maroua da ke zama fadar gwamnatin Jihar Arewa Mai-nisa n akasar Kamaru.

Gwamnan jihar Mijiyawa Bakary ya tabbatar da faruwar lamari, kuma akwai wasu mutanen da suka samu raunika. Ana danganta harin da tsagerun kungiyar Boko Haram na Najeriya, wadanda suka yi kaurin suna wajen hare-haren da ke hallaka mutane a arewacin Najeriya da wasu kasashe makwabta na Kameru, da Jamhuriyar Nijar, da kuma Chadi.