Hangari ta killace iyaka da Sabiya | Labarai | DW | 15.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hangari ta killace iyaka da Sabiya

Daruruwan bakin haure sun fara watangariri a kan yakar Hangari da Sabiya sakamakon matakin da gwamnatin Hungari ta dauka.

A kasar Hangari an samu rudani da rashin tabbas bayan rufe kan iyaka saboda dakile kwararan bakin haure daga iyakar kasar da Sabiya. Karkashin sabuwar dokar da kasar ta kaddamar duk bakon da ya shiga cikin kasar ba tare da takardun izini ba zai fuskanci tuhuma. Rahotanni sun nuna cewa mahukunta sun tsare daruruwan bakin haure wadanda suka karya izinin shiga kasar, bayan fara aikin da dokar ta-baci.

Tuni ministan Aleksandar Vulin kula da walwala a gwamnatin Sabiya ya bukaci kasar ta Hangari ta sake bude iyakar domin bakin haure da 'yan gudun hijira su wuce. Hukumar kula da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa saboda rashin cimma matsaya tsakanin kasashen Turai kan yadda za a raba masu neman mafaka tsakanin kasashen na kungiyar Tarayyar Turai. Sigmar Gabriel mataimakin shugaban gwamnatin Jamus ya ce kasashen Turai sun ba da kunya bisa gaza warware matsalar masu neman mafaka tsakanin kasashen.