Hamas ta yi baranar yin fatali da shirin tsagaita wuta a Zirin Gaza | Labarai | DW | 04.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas ta yi baranar yin fatali da shirin tsagaita wuta a Zirin Gaza

Kungiyar Hamas ta masu kishin Islama ta yi barazanar janyewa daga shirin tsagaita wuta da aka cimma makon jiya tsakanin Isra´ila da Falasdinawa a Zirin Gaza. Hamas ta ba da dalilin yin haka da ci-gaba da matakan sojin da Isra´ila ke dauka a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan. Harin baya bayan nan da Isra´ila ta kai a yankin ya yi sanadiyar mutuwar wani saurayi dan shekara 15 da haihuwa, wanda sojin Bani Yahudun suka harbe shi lahira. A jiya lahadi wata roka da aka harba daga Zirin Gaza ta fadi a cikin Isra´ila. Rokar ita ce ta 15 da Falasdinawa suka harba cikin Isra´ila tun bayan fara shirin tsagaita wutar.