Gwamnatin Ukraine ta dakara da janye manyan makamai daga fagen daga | Labarai | DW | 23.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Ukraine ta dakara da janye manyan makamai daga fagen daga

A karshen mako gwamnati da 'yan aware sun cimma shirin janye makamai karkashin yarjejeniyar amar yadda shirin zaman lafiya ta Minsk.

Gwamnatin Ukraine ta dage shirin janye manyan makamai daga fagen daga da ke gabashin kasar. Kakakin gwamnati a birnin Kiev ya ce ci-gaba da harbe-harbe da 'yan aware masu goyon bayan Rasha ke yi shi ne dalilin daukar wannan mataki. A karshen mako gwamnati da 'yan tawayen sun ba da sanarwar cimma wata yarjejeniyar janye makamai daga fagen daga kamar yadda shirin samar da zaman lafiya na birnin Minsk ya tanada. Tun farko masu lura da al'amura sun yin zargin cewa 'yan awaren sun amince su janye daga fagen daga da ke yamma don su karfafa ikonsu a gabas a kokarin da suke na kai farmaki kan birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa. A kuma halin da ake ciki gwamnatin Jamus ta nuna damuwa game da fadan da ake ci gaba da gwabzawa a gabashin Ukraine.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu