Gwamnatin Sudan ta hana shugaban hukumar agaji ta MDD kai ziyara Dafur. | Labarai | DW | 03.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Sudan ta hana shugaban hukumar agaji ta MDD kai ziyara Dafur.

Shugaban hukumar agaji ta majalisar dinkin duniya Jan Egeland yace gwamnatin Sudan ta hana masa kai ziyarar gani da ido yankin Dafur domin hana shi ganin mawuyacin hali da jamaá ke ciki a yankin. Jan Egeland, ya danganta lamarin da cewa bai da maraba da abin da ya wakana a shekarar 2004 inda aka hana jamián agaji isa ga yankin Dafur domin bada gudunmawar abinci ga jamaá. Yace wannan na daga cikin irin matsalolin da maáikatan agaji ke fuskanta a kullum a kokarin su na taimakawa jamaá kimanin miliyan uku dake tsananin bukatar abinci a Dafur. Jamiín na majalisar dinkin duniya wanda ke rangadin kasashen nahiyar Afrika, yace jamaá da dama sun tagaiyara a sakamakon tarzomar da ta auku a garin Gereida dake hannun yan tawaye a kusa da lardin Dafur. Majalisar dinkin duniya ta yi kakkausar suka ga gwamnatin Sudan a dangane da hana Jan Egeland zuwa yankin na Dafur. Babu dai wani martani daga gwamnatin Sudan.