Goodluck Jonathan zai yi takara a 2015 | Labarai | DW | 23.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Goodluck Jonathan zai yi takara a 2015

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana aniyarsa ta sake neman kujerar shugaban kasar a zabukan da za su gudana a watan Fabrairun shekarar da ke tafe.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito wata majiya a fadar shugaban kasar na cewa shugaban ya ambata hakan ne bayan da ya gana da jiga-jigan jam'iyyarsa ta PDP a yau (23.10.2014), inda ya jinjina musu dangane da amincewar da suka nuna masa tun a baya na ya nemi wannan kujera.

Shugaba Jonathan ya kuma shaidawa shugabannin jam'iyyar tasa cewar zai sayi fom din shiga takara kafin wa'adin da aka diba na sayan fom din ya cika cikin mokon gobe.

A farkon watan Nuwamban da ke tafe ne dai ake sa ran shugaban zai bayyana wannan aniya tasa a hukumance gaban 'ya'yan jam'iyyar a wani taro da su gudanar a Abuja.