Gasar kwallon kafa ta duniya: Tarihi da misalai cikin hotunan barkwanci
Jamus ta zartar da 'yan wasa da zasu wakilceta a gasar cin kofin duniya ta 2018. Abun mamaki, Leroy Sane ba ya cikinsu. Sai dai hakan ba abun mamaki ba ne bisa tarihi, inji mai zanen barkwanci German Aczel a littafinsa.
1930: Gatana gatananku.....
An gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta farko a kasar Uruguay a 1930. Mafi yawan kungiyoyin kwallon kafar sun fito ne daga yankunan Arewaci da Tsakiya da kuma Kudancin Amirka; tawagar kungiyoyi hudu ne kawai suka wakilci Turai. Mai masaukin baki ta doke abokiyar hamayyarta Ajentina a gasar karshe da ci 4-2. Zanen hoton Aczel na nuna shugabannin 'yan wasan na jagorantarsu zuwa cikin fili.
1954: Abin mamaki a Bern
An gudanar da gasar kwallon kafa ta duniya ta farko bayan yakin duniya na biyu a kasar Switzerland. A wasannin sharar fage Hungary ta doke Jamus da ci 8-3. Amma labarin ya sauya a wasan karshe na gasar, inda Jamus ta doke Hungary da ci 3-2. Lokacin ne ta zama zakaran gasar cin kofin duniyar a karon farko. Ana iya ganin hotunan Fritz Walter da mai horaswa Sepp Herberger a kan kafadun 'yan kwallo.
1966: Guda daya tilo
Ingila da ake wa kallon tushen kwallon kafa, ta samu nasarar zama zakaran duniya a fagen kwallo ne sau daya kacal a 1966, lokacin da aka yi gasar a kasar. A wasan karshe Ingila ta doke Jamus da ci 4-2. Sai dai har yanzu akwai sarkakiya dangane da kwallon da Ingila ta jefa a raga a mintuna na 101, cikin karin lokacin wasa.
1970: Pele ya samu daukaka sau uku
A 1970 Brazil ta zama zakaran gasar kwallon kafa ta duniya a karo na uku. Pele da ke zama daya daga cikin taurarin kwallon kafa na karni na 20, ya jagoranci tawagar 'yan kwallonsa da nasarar 4-1, bayan da Brazil ta samu nasarar jefa kwallo a raga har sau 19 cikin wasannin shida. Jamus ta Yamma ta zo na 3 bayan doke Uruguay da ci daya da nema. Lokacin ne aka fara kallon wasan kwallo ta Talabijin.
1974: Karawar Beckenbauer da Cruyff
Gasar kwallon kafa ta duniya ta farko a Jamus, ta samu halartar fitattun 'yan wasa. Zakaran wasa na Jamus Franz Beckenbauer ya kara da fitaccen dan wasa na Netherland Johan Cruyff, kana Jamus ta Yamma ta kara da bangaren Gabashi. A wasan karshe, Jamus ta doke Netherland da ci 2-1, inda fitaccen dan wasa Gerd Müller ya jefa kwallon da ya tabbatar da wannan nasara.
1986: Ikon Allah
Har yanzu ana tunawa da wasan da aka yi a Mexico saboda irin bajintar da zakaran wasan Ajentina, Diego Maradona, ya nuna, wanda ya baiwa kasar nasarar cin kofin a karo na biyu. Maradona ya jefa kwallo mai ban mamaki cike da sarkakiya cikin raga, har da wanda ya yi amfani da hannunsa. Buge 'yan wasan Ingila biyar a kan hanyarsa ta sa kwallon, ya kasance cikin tarihi.
1990: Harin tofa yawu
Jamus ta yi bikin nasarar daukar kofin kwallon kafa ta duniya a karo a na uku a Italiya, bayan ta doke Ajentina da ci daya da nema. Sai dai abin da za a iya tunawa shi ne, lokacin da dan wasan Netherland Frank Rijkaard ya tofawa dan wasan Jamus Rudi Völler yawu, a lokacin da sabani ya shiga tsakaninsu a minti na 16. Hakan ya tilasta 'yan wasan biyu barin filin wasa.
2006: Zidane ya rude
An yi ta bukukuwa na gasar kofin duniya a wannan shekara a Jamus, kasar da ta karbi bakoncin wasannnin da aka yi wa lakabi da "almara a lokacin bazara." A wasan karshe Italiya ta yi nasara kan Faransa a bugun fenariti. Abin muni da ya auku lokacin karawar shi ne bugu da ka da kaftin din Faransa Zinedine Zidane ya yi wa dan wasan Italiya Marco Materazzi. An ba shi jan kati.
2010: Nasarar salon wasa na "Tiki-taka"
A Afirka ta Kudu, kasar Spaniya ta yi galaba a kan abokanen karawarta da salon wasa na "Tiki-taka". A wasan karshe Spaniya ta doke kasar Netherlands da ci 1-0, inda ta yi bikin nasara mafi girma da ta taba samu a tarihinta na wasan kwallon kafa. Andreas Iniesta ya ci mata kwallon a karin lokaci na wasa. Jamus ta zo ta uku bayan ta doke Uruguay da ci 3-2.
2014: Sarkin murza kwallo
Gwarzon wasan da ya gabata wanda ya gudana a kasar Brazil, shi ne dan wasan kasar Ajentina Lionel Messi. Godiya a gareshi, Ajentina ta kai wasan karshe, inda ta kara da kasar Jamus, wadda ta lallasa Brazil mai karbar bakonci da ci 7-1 a wasan kusa da na karshe.
2014: Kungiyar kwallon kafa mai karfi
Kimanin 'yan kallo dubu 75 suka cike filin wasa na Maracana da ke birnin Rio de Janeiro don kallon wasan karshe tsakanin Jamus da Ajentina. Jamus ta yi nasara da ci 1-0 a karin lokaci, a kuma karo na farko, wata kungiyar nahiyar Turai ta yi nasarar cin kofin a wata kasa ta Kudancin Amirka.
2018: Takaddama kan kofi
Rasha ke daukar bakoncin gasar ta wannan shekara, a wani zabi mai cike da takaddama yayin badakalar cin hanci a cikin hukumar FIFA da zargin amfani da kwayoyi masu kara kuzari. Rasha ta yi wasan farko da Saudiyya a ranar 14 ga watan Yuni a birnin Mosko. A ranar 15 ga watan Yuli za a yi wasan karshe shi din ma a filin wasa na Luzhniki da ke Mosko.
Zagaye na ban dariya cikin tarihi
Kofin duniya daga 1930 zuwa 2018, tarihi a zanen barkwanci da kamfanin Edel Books ya wallafa. Littafin ya yi bayani daki-daki na lokutan da ba za a mantawa da su ba na tarihin shekaru 88 na gasar kofin duniya, da zanen barkwanci da rubutu na nishadantarwa. Bangon littafin ya nuna fitattun 'yan wasa na gasar 2018, cikinsu akwai Cristiano Ronaldo, Manuel Neuer, Lionel Messi da kuma Neymar.
Mai zanen barkwanci
German Aczel, dan Ajentina, shi ne dan fasahar da ya yi zanen a littafin. Ya fara sana'arsa a garinsu na haihuwa wato Buenos Aires, inda ya yi aiki da mujallar wasannin motsa jiki ta El Grafico. Ya zo Jamus da zama yana da shekaru 26, yanzu haka yana zaune a birnin Munich. Yana aiki da mujallar kwallon kafa ta Birtaniya wato FourFourTwo.