Ganawa kan kawo karshen rikicin Ukraine | Labarai | DW | 03.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawa kan kawo karshen rikicin Ukraine

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya yi wata ganawa da takwaransa na Ukraine Petro Poroshenko kan rikicin gabashin Ukarine tsakanin dakarun gwamnatin da 'yan aware.

Kamfannin dillancin labaran Rasha na Interfax ya rawaito mai magana da yawun shugaba Putin Dmitry Peskov na cewar shugabannin biyu sun yi ganawar ce ta wayar tarho inda suka amince da wasu matakai na samun mafita dangane da kawo karshen rikicin.

Rikicin Ukraine din wanda ya dau lokaci ana gudanar da shi na cigaba da daukar hankalin kasashen duniya musamman ma dai Amirka da wasu kasashen Turai wanda suka kakabawa Rasha takunkumi a wani mataki na ganin ta sassauta matsayin da ta dauka kan rikicin.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu