1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya : Kyamar 'yan mulki na karuwa

November 8, 2021

A yayin da ake shirin gudanar da zabe kasa da watanni 18, hakurin talakawan Najeriya na dada karewa sakamakon jerin hare-hare da ke karuwa a sassan kasar.

https://p.dw.com/p/42kKl
Nigeria Feier 60 Jahre Unabhängigkeit
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Daga Kano zuwa Sokoto bayan Rivers da jihar Gombe, shugabannin siyasa na ji a jiki sakamakon boren ba-zata da kuma ke dada daukar hankali cikin kasar a halin yanzu. Ba sabun ba ne a cikin kankanen lokaci ihu ya zuwa jifa ga shugabanni tun bayan samun sauyin da 'yan kasar ke fata, to sai dai kuma kasa da shekara daya da rabi ya zuwa karshen wa'adin mulkin a matakai dabam-daban, tarrayar Najeriya na fuskantar sabon tsarin lakuce hankalin yan mulkin dake kara fitowa fili cikin kasar a halin yanzu.

Cikin kasa da tsawon mako daya an kalli ihu a Kano ko kuma kokari na yagun riga a Sokoto ko bayan asarar rai a Gombe duk dai a cikin rikicin da ke daukar launi iri-iri a halin yanzu. Sai dai ra'ayi na banbanta cikin kasar a tsakanin masu yiwa boren kallon batun siyasa, ya zuwa masu yi masa kallon alamu na isar talakawa ya zuwa bango.

Cartoon Nigeria Politik Lage

Engr Buba Galadima da ya share shekaru cikin fagen siyasar Najeriya na kallon sababbin hare-haren da idanu na aika babban sako ga masu mulki a matakai daban-daban cikin tarrayar Najeriyar.

Karin Bayani: kalubalen Najeriya bayan shekaru 61 da 'yancin kai

Adalcin 'yan mulki ko kuma tada kayar bayan talakawa, sabbabin rigingimu da ke zuwa kasa da wattani 18 da babban zabe a Najeriyadai na zaman irinsu na farko tun bayan sauyin da ya kare mulki na masu tsintsiyar kasar shekaru shida baya. Kuma a tunanin Dr Faruk BB Faruk da ke sharhi cikin siyasar tarrayar Najeriya, abun da ke faruwa cikin fagen siyasar kasar yanzu, na zaman alamun karshen mulki dake tabbatar da halin kowa.

Najeriyar na kara matsawa ya zuwa zabe ne a cikin halin rashin tsaro dama talaucin annobar Corona. Muhimman batutuwa guda biyun da ke shirin tasiri cikin fagen siyasa a kasar yayin zabukan da ke tafe, batutuwan da wasu masu taka rawa a fagen siyasa irin su Comrade Sa'idu Bello ke cewa na tunzura talakawa.