1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigingimu a zaben shugabannin jam'iyyu na jihohin Najeriya

Uwais Abubakar Idris MNA
October 18, 2021

A Najeriya rigingimu sun mamaye zabubbukan shugabannin manyan jam'iyyun kasar a jihohin kasar da dama, a yanayin da ke nuna halin da 'yan siyasa da ma jam'iyyar ke ciki wanda ke da tasiri ga dimukuradiyyar kasar.

https://p.dw.com/p/41pN3
Nigeria Benin City | Edo State Wahlen | Godwin Obaseki gewinnt
Hoto: Olukayode Jaiyeola/picture-alliance/dpa

Zabubbukan shugabannin jam'iyyar ta APC a matakin jihohi sun bar baya da kura, domin kuwa duk da daukan dogon lokaci da aka shirya masu har ma da dage lokacin farko da aka so yin zabubbukan, an rabu dutse hannun riga a  jihohi da dama irin su Kano, Bauchi da ma Neja. Mallam Sabo Imam dan siyasa ne da ya sa ido a kan abin da ya faru.

"Ni da ma na hango faruwar wannan al'amari. A sama da Maimala Buni ya yi kokarinsa ya kawo gwamnoni kuma ya kawo manyan mutane 'yan PDP, amma a kasa a gida mutane suna nan suna ji haushin wannan jam'iyya. Ka da su manta yanzu kasuwar karshe ake ci."  

Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

Amma bisa ga abin da ya faru an ya 'yan siyasar sun koyi darasi daga abin da ya faru? Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa ne da ke jami'ar Abuja.

"Ba su koyi wani darasi ba, kuma har yanzu ba su ma kama hanyar wanzar da dimukuradiyya ta cikin gida ba. A kusan jihohin da aka samu rikita-rikita da ma wadanda ba a samu ba, Abin da ya faru wasu gwamnoni masu ci yanzu da tsofaffin gwamnoni sun kokari su yi karan tsaye su yi kane-kane a jam'iyyun ko da kuwa hukumomin jam'iyyun suna so ko ba sa so, kua ta hanyoyi wadanda ba na dimukuradiyya ba."

A yayin da kurar rigingimun jam'iyyun ta tirnike sama, an bar 'ya'yan jam'iyyar irin su Hassan Sharrif daya daga cikin 'yan takara a jihar Bauchi da ya ce "an dai yi watsi da duk wata ka'ida da aka shimfida".

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

A jam'iyyar PDP ta 'yan adawa ma dai an fuskanci tashin-tashina a wasu yankuna wajen zabubbukan shugabannin jam'iyyar a matakin jihohi. Shin mene ne hatsarin wannan karfa-karfa ga jamiyyun da dimukurdiyar Najeriyar? Har ila yau ga Dr Abubakar Umar Kari.

"Abin da ya faru yana da hatsarin gaske ga dukkan jam'iyyun siyasar Najeriya da harkar dimukuradiyyar kasar gaba daya."

Jam'iyyar APC dai ta fitar da sanarwa a Litinin nan, wacce James John ya sanyawa hannu, inda jam'iyyar ta ce tarurrukan da jami'ar da ta kaddamar aka ba su aiki suka zabi shugabanni ne kadai za ta amince da su.

Masharhanta na bayyana tsoron abin da zai faru a babban taron manyan jam'iyyun da suke shirin gudanarwa a nan gaba kadan, inda za su zabi sabbin shugabanninsu. A kan ce Jumma'ar da za ta yi kyau dai tun daga ranar Laraba ake gane ta.