EU: Za mu tallafa wa al′ummar tafkin Chadi | Labarai | DW | 05.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU: Za mu tallafa wa al'ummar tafkin Chadi

Hukumar Tarayyar Turai ta sanar da aniyarta ta bada karin wani tallafi ga al'ummar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a yankin tafkin Chadi.

Hukumar ta ce akwai kudade kashi-kashi da suka kama na Euro miliyan tara, da miliyan biyu, da miliyan daya da rabi da dukanin su za a tattara domin taimaka wa mutanen da ke cikin Najeriya, Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar. Da yake magana kan abubuwan da suka gane wa idanunsu a yankunan na tafkin Chadi yayin da ya kai wata ziyara a watan da ya gabata, Christos Stylianides, babban jami'in Tarayyar Turai mai kula da harkokin agaji, ya ce sun ga miliyoyin 'yan gudun hijira kuma a game da masu neman abun da za su ci lamarin na kara ta'azzara.

wani mataki na amsa kiran da kungiyoyi masu zaman kansu da ke ayyuka a yankunan da 'yan gudun hijiran suke, jami'in kula da agajin na Tarayyar Turai ya ce, tallafin na gaggawa zai kasance ne kayayakin abinci mai gina jiki, ruwan sha, tsaftace wurare da kuma kiwon lafiya.