EU ta bukaci tsawaita takunkumi kan Rasha | Labarai | DW | 26.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta bukaci tsawaita takunkumi kan Rasha

Shugaban hukumar hadin kan kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk, ya bukaci kasashen duniya masu karfin tattalin arziki wato G7 da kada su goyi bayan janye takunkumi kan kasar Rasha bisa rikicin Ukraine.

Brüssel Donald Tusk zu Brexit (Reuters/Y. Herman)

Shugaban EU, Donald Tusk

Tusk ya bayyana wannan mataki ne a yayin da shugabannin kasashe mafi karfin tattalin ariki a duniya ke ganawa a yankin Sicilya na kasar Italiya. To sai dai Amirka bata fito karara ta bayyana matakinta kan wannan yunkuri ba.

A shekarun bayane kungiyar tarayyar Turai da gwamnatin tsohon shugaban Amirka Barack Obama, suka kakabawa Rasha takunkumi kan yadda ta mamaye yankin Kirimiya dama iza wutar rikici tsakanin dakarun gwamnati da masu adawa a gabashin Ukraine.

To sai dai babu tabbacin ko sabon shugaban na Amirka Donald Trump zai mutunta takunkumin ko a a, ganin yadda yake fama da Rasha akan zargin kutsen yanar gizo a lokacin zaben kasar a bara.