Erythrea ta kori kungiyoyi masu kansu 3 na kasar Italia | Labarai | DW | 16.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Erythrea ta kori kungiyoyi masu kansu 3 na kasar Italia

Gwamnatin Eryhtrea ta umurci wasu kungiyoyi 6, masu zaman kansu na Italia da su ka tattara yana su yana su ,su hita daga kasar.

Sanarwar da gwamnatinya hiddo ta bayana masu cewa bas u cika sharradu aiki ba a kasar Erythrea.

A shekara da ta gabata gwamnatai ta shinfida wasu ka´idoji wanda cuilas sai kungiya ta cika su kaminta samu dammar aiki a wanna kasa.

Wannan ka´idoji sun hada, cenza izinin aiki a ko wace shekara, da bada tallafi na dalla dubu 840, ga kungiyoyi masu zaman kansu, na cikin gida, da kuma kimanin dalla million daya da rabi ga kungiyoyi masu zaman kansu, na kasa da kasa.

Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Erythrea ta amince da kungiyyoyi 17, su ci gaba da aiki, a tsawan shekara bana,a yayin da wasu 10, da ke cikin jiran izini.