1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyautar 'yancin fadar albarkacin baki

Marie Sina AH/LMJ
May 4, 2021

Tobore Ovuorie 'yar jarida mai binciken kwakwaf 'yar Najeriya ta lashe lambar yabo kan fadin 'yancin albarkacin baki ta tashar DW ta shekara ta 2021.

https://p.dw.com/p/3sxCN
Freedom of Speech Award 2021 | Preisträgerin Tobore Ovuorie aus Nigeria
Tobore Ovuorie 'yar jaridar da ta lashe kyautar 'yancin fadar baki ta tashar DWHoto: Elvis Okhifo/DW

Tobore Ovuorie ta yi ayyukan bincike masu hadari ga rayuwarta, kasancewarta guda cikin manyan 'yan jaridu masu binciken kwakwaf da bin diddigi a Najeriya. 'Yar jaridar tana da burin tsage gaskiya da kuma bankado boyayyun lamari. A shekarar 2013, Tobore Ovuorie ta yi kasadar rayuwa na aikin karuwanci na tsawon watanni 7 dan bankado yadda ake safarar mata dan karuwanci da kuma sayar da sassan jikin bil'adama: "Wannan shi ne abin da na zaba na yi a sauran rayuwata. Tsayin daka ga marasa iko ta hanyar rubutu. Aikin jarida fannin binciken kwakwaf shi ne burina."

Karin Bayani: DW ta karrama 'yar jarida Hernandez

Ayyukan Tobore Ovuorie mai shekaru 33 a duniya na basaja a matsayin mai aikin karuwanci, ya taimakawa gwamnatin Najeriya gano yadda ake safarar mata daga kasar zuwa wasu kasashen ketere, sai dai ta sha da kyar bayan da aka yi mata fyade da cin zarafi da dama: "Rayawar mutane da dama ta kubuta saboda labarin. Yanzu zan iya bacci har da minshari, a gareni wannan yana da muhimmanci."

eu2020 Medienkonferenz Peter Limbourg Archivbild
Shugaban tashar DW Peter LimbourgHoto: picture-alliance/dpa/H. Kaiser

Shugaban tashar DW Peter Limburg, ya ce kwarin gwiwar Tobore a aikin jarida, shi ya ba ta damar cin kyautar da tashar ke bayar wa duk shekara kan 'yancin fadin albarkacin baki a bana: "Ina ganin lambar yabo kan fadin albarkacin baki na taimakon 'yan jaridu a yanayi mara kyau wajen yin aikinsu. Yana nuna gaskiya a aikinmu kuma wani abu ne da ke nuna kwarin gwiwar aikin jarida na da muhimmanci a garemu da al'ummarmu. Ina ganin mace ce mai kwarin gwiwa kuma ina ganin irin wanna kyautar za ta taimaka wa aikinta, da kuma tsaronta."

Karin Bayani: Raif Badawi ya samu lambar yabo daga DW

Bayana wannan aiki na kasada, labarin Tobore Ovuorie ya ja hankalin manyan kamfanonin shirya fina-finai a dunyia kamar Netflix. Wannan ya sa sauran 'yan jaridu kamar Anas Arma Ya'u Anas da ya yi fice wajen kwarmata bayanan kwakwaf daga Ghana ke cewa: "Wani zai yi tunani aikin jaridar Tobore zai zo karshe. Amma ta bai wa kowa mamaki bayan da ta dawo da karfinta. Ta fuskanci kalubale amma domin samun waraka ta dawo da karfi, shi ma abin burgewa ne."

Yanzu haka dai Tobore 'yar jaridar Najeriya da ta lashe kyautar lambar yabo ta DW kan fadin albarkacin baki a 2021, na fatan aikinta ya zama madubi ga sauran mata wajen samun kwarin gwiwa.