Raif Badawi ya samu lambar yabo daga DW | Zamantakewa | DW | 25.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Raif Badawi ya samu lambar yabo daga DW

Raif Badawi mai kimanin shekaru 31 ɗan asilin ƙasar Saudiyya ya samu lambar daga tashar DW saboda fafutukarsa ta kare hakkin bil Adama ta hanyar rubuce-rubucen da yake yi ta intanet

Tashar Deutsche Welle ta bai wa Raif Badawi ɗan ƙasar Saudiya mai rubutu a shafukan Internet lambar yabo kan faɗin albarkacin baki. Badawi yanzu haka ana tsare da shi a gidan kurku kuma shi ne mutum na farko da ya samu wannan lamba ta yabo daga tashar DW.

DW ta gamsu da fafutukar da Raif Badawi ke yi na kare hakkin jama'a

Peter Limbourg

Shugaban Tashar DW Peter Limbourg -

Tashar ta DW dai ta ba da wannan lambar yabo ce ga Raif Badawin mai shekaru 31 saboda jajircewar da ya yi wajen ganin an samu kyautatuwar al'amuran kare hakkin ɗan Adam a ƙasar Saudiyya, da kuma yancin faɗar albarkacin baki. Da yake magana a lokacin bada wanan sanarwa daraktan DW Peter Limbourg ya ce sun ba da wannan lambar girma ta yabo domin ƙara jan hankali duniya a kan tsaron da ake yi wa Raif Badawi domin hukumomin Saudiyya su gaggauta sako shi.

'' Kuzari da hamzarin da Raif Badawi ya nuna a cikin ƙasa musammun kamar Saudiyya na neman ganin an samu yanci faɗar albarkacin baki shi ne abin da ya ɗauka mana hankali muka ba shi wannan lamba ta yabo a kan aikin da ya dogara a kansa na samun sauyi.''

Kotu a ƙasar Saudiyya ta yanke wa Badawin hukuncin ɗaurin shekaru goma na zaman gidan yari a cikin watan Mayu na shekara ta 2014 tare da yi masa bulala ɗari da kuma cinsa tara ta kuɗaɗe misali Euro dubu ɗari biyu.

Tun a ranar 9 ga watan Janairu na wannan shekara an riga an yi masa bulala 50 a benar jama'a kuma a shirya a gaba a yi masa wata bulalar 50 amma sai aka ɗage hukuncin.Hakan kuwa ya biyo bayan da gwamnatin ta zargeshi da yin ɓatanci a kan addini musulunci.Tun da farko dai ya fice ya bar ƙasar amma kuma ya dawo daga bisani kafin a kamashi a shekaru 2012.

Maidakinsa Ensaf Haide ta yi marhabin da lambar yabon

c Frau Blogger Raif Badawi

Maidakin Raif Badawi Peter Limbourg -

Ensaf Haider maiɗakin Badawi wacce ta tsere a shekarun 2013 tare da ya'yansu guda uku zuwa Kanada inda ta samu mafuka ta siyasa ta yi tsokaci a kan batun

'' Abin kunya ne gwamnatin Saudiyya ta ci gaba da tsare mijina har ya zuwa wannan lokaci, yancin faɗar albarkacin baki wani babban yunƙurin na ci gaban dimokaraɗiyya a cikin ƙasa.''

A bisa shafinsa dai na Blogs Badawi yana faɗikar da 'yan siyasa na Saudiyya dangane da irin abubuwan da ke faruwa a ƙasar. Misali wani shafin da ya bayyana wanda ya jan hankalin duniya shi ne irin yadda 'yan sanda ƙasar ke galazawa jama'a, sannan kuma ya kamanta Saudiyyar da cewar maɓuya ce ta yan t'adda. Wannan dai shi ne karon farko da tashar DW ta ba da wannan lambar yabo ta yancin faɗar bakin albarkacin jama'a wanda zai shiga rukunin gasar ƙasa da ƙasa,ta Blogs wanda a ƙarshe za a tattara gwanayen harkokin na Blogs domin karamasu da kyautar a cikin watan Yuni da ke tafe a taron kafafen yaɗa labarai na duniya wanda DW ke shirya a kowacce shekara a nan birnin Bonn.

Sauti da bidiyo akan labarin