Diplomasiyya ita ce Masalaha ta warware rikicin Iran | Labarai | DW | 12.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Diplomasiyya ita ce Masalaha ta warware rikicin Iran

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kiran nuna dattako tare da samun hanyoyi na diplomasiyya domin kawo karshen takaddamar makamashin nukiliyar kasar Iran, tana mai cewa akwai bukatar kasashen duniya su kaucewa irin rarrabuwar kawuna da aka fuskanta a lokacin da Amurka ta afkawa Iraqi a shekarar 2003. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta ce za ta yi iya bakin kokarin ta domin jawo hankalin kasashen duniya su fuskanci manufa guda, da kuma baiyanawa kasar Iran abin da zai yiwu da kuma wanda ba zai yiwu ba. Angela Merkel ta baiyana hakan ne a yayin da ta ke ganawa da shugaban kasar Masar Hosni Mubarak a birnin Berlin. Shugabara ta ce ta yi farin ciki da hukumar makamashin nukiliyar IAEA ta gabatar da batun ga kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya. Tuni dai kwamitin sulhun ya fara nazarin rahoton na IAEA inda ta ke duba hanyoyin da suka dace na shawo kann kasar Iran ta dakatar da shirin ta na makamashin nukiliya.