Dangantakar Jamus Da Poland | Siyasa | DW | 28.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantakar Jamus Da Poland

A ganawar da suka yi jiya litinin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da takwaransa na kasar Poland Marek Belka sun yi fatali da maganar diyyar yakin duniya na biyu dake addabar yanayin dangantakar kasashen biyu

Matsalar dake akwai a dangantakar Jamus da Poland shi ne kasancewar al’amuransu na tafiya ne ta fuskoki biyu. Da farko akwai matsayi na gwamnati, inda al’amura ke tafiya salin alin ba tare da wata tangarda ba. Dukkan sassan biyu, a tarurrukan da suka saba gudanarwa akai-akai ko dai a Berlin ko a Warsaw, sun sha nanata batu a game da yadda ake dada samun kyautatuwar dangantakarsu. To sai dai ayar tambaya a nan shi ne ko irin wannan alakar a hukumance zata wadatar wajen kyautata yanayin dangantakar tasu. Domin kuwa da zarar an rabu da fadar mulki za a tarar da matsaloli masu yawan gaske dake hana ruwa gudu wajen dinke barakar da ta samu tsakanin Jamus da Poland sakamakon yakin duniya na biyu. Ita kanta majalisar dokokin kasar Poland, daga baya-bayan nan ta taimaka wajen kara rura wutar sabanin, inda take neman diyyar barnar yakin daga Jamus. Kafin hakan ya faru sai da wata gamayya ta Jamusawan da aka kora daga kasar Poland suka yi kurarin daukaka kara gaban kotun Turai domin neman diyyar kadarorinsu da aka kwace a yankunansu na asali dake karkashin mulkin Poland. An yi tsawon watanni da dama maganar tabon yakin duniya na biyu na gurbata yanayin dangantaku tsakanin kasashen biyu. Wannan maganar ta fi tsamari a kasar Poland. Domin kuwa a yayinda a nan Jamus wasu 'yan tsiraru ne dake tattare da ra’ayi irin na mazan jiya ke yayata wannan batu, a can kasar Poland kusan illahirin al’umar kasar ne ke da ra’ayin neman diyya daga Jamus, kuma kafofin yada labarai na kasar kai taimaka wajen kara sosa wa jama’a daidai inda ke musu kaikai. Ta la’akari da wannan takaddama da ta ki ci ta ki cinyewa, dukkan shuagabannin gwamnatocin kasashen biyu, Schröder da Belka, a lokacin ganawarsu ta jiya litinin, suka tsayar da shawarar kafa wani kwamitin kwararrun masana shari’a domin shawo kan matsalar diyyar. Belka daidai da Schröder yayi fatali da maganar diyya, wadda ya ce bata taso ba a wannan marra da muke ciki yanzun. Dukkan shuagabannin biyu dai sun yi iyakacin kokarinsu wajen lafar da kurar rikicin, amma abin ta kaici shi ne za a ci gaba da wannan cece-kuce dake taimakawa wajen gurbata yanayin dangantaku tsakanin Jamus da Poland kuma ta la’akari da haka muna iya cewar har yau da sauran tafiya mai nisa kafin a samu sararawar al’amura a dangantakar kasashen biyu.