Dakarun Cadi sun kori wani harin Boko Haram | Labarai | DW | 11.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Cadi sun kori wani harin Boko Haram

Da safiyar wannan Larabar ce 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari ga dakarun kasar Chadi da a halin yanzu suke rike da Gamborun Ngala da ke arewa maso gabashin Tarayyar Nageriya

Sai dai hakarsu bata cimma ruwa ba domin kuwa dakarun sojan kasar ta Cadi sun fatattakesu a cewar wata majiya ta soji da ta sanarwa kanfanin dillancin labaran Reuters. Daya daga cikin sojojin na Cadi ya sanar cewa takwas daga cikin dakarunsu sun ji rauni, amma kuma sun samu ragargaza motoci uku daga cikin 14 da 'yan boko haram din suka kawo harin da su.

A yammacin jiya Talata (10.02.2015) ma dai an ji karan manyan bindigogi a yankin Nguigmi na Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Najeriya. Tuni gwamnatin ta Nijar ta ayyana dokar ta baci a jihar Diffa ta tsawon kwanaki 15 don baiwa jami'an tsaron damar shiga dukkan gidajan da suke da konkonto a kansu. Daga bangaren Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan zai yi wani jawabi da yammacin wannan Laraba kan batun na tsaro da ya haddasa dage zabe Najeriya.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu