Cutar Corona ta kashe wani mutun a Jamus | Labarai | DW | 16.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Corona ta kashe wani mutun a Jamus

Mutumin wanda dattijo ne dan shekaru 65 ya rasu ran shida ga watan Yuni bayan kamuwa da cutar a lokacin wani balaguro da ya yi a kasashen Larabawa.

A kasar Jamus hukumomin kiwon lafiya sun tabbatar da mutuwar wani dattijo dan shekaru 65 da haihuwa a sakamakon kamuwa da cutar nan ta matsalar nunfashi da ake kira Corona. Hukumomin kiwon lafiyar kasar ta Jamus sun ce mutumin wanda ya rasu tun a ranar 6 ga watan Yuni a wani gidan asibitin yammacin kasar ya kamu da cutar ne lokacin wani balaguro da ya yi a kasashen Larabawa inda ya ziyarci wata kasuwar dabbobi.

Hukumomin lafiyar kasar ta Jamus sun ce sun dauki matakin gudanar da binciken lafiyar mutane kimanin 200 da suke da mu'amala da shi lokacin kamuwarsa da cutar kafin a kwantar da shi kuma binciken ya nunar da cewa ba dayansu da ya kamu da cutar.

Kawo yanzu dai wannan cuta ta Corono wacce ke halaka kashi 35 daga cikin 100 na wadanda suka kamu da ita a cewar hukumar lafiya ta duniya, ba ta da wani magani. Mutane sama da 400 ne ta hallaka kawo yanzu a kasashen Saudiyya da Koriya ta Kudu.