Cika shekaru 30 na karshen gaba a Jamus | Labarai | DW | 19.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cika shekaru 30 na karshen gaba a Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firaministan Hangari Viktor Orban sun yi bukin zagayowar cika shekaru 30 da kasar Hangari ta bude kofofinta ga 'yan Jamus ta Gabas da ta Yamma.

Shugabannin biyu sun gudanar da bukuwan ne a birnin Sopron mai dadadden tarihi, inda Jamusawa na Gabas fiye da 600 suka keta iyakar Ostiriya domin gujewa Jamus ta Yamma a ranar 19 ga watan Agustan shekara ta 1989, matakin da ya bai wa 'yan kasar da dama karsashin shiga gwagwarmayar rusa katangar Berlin.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce da ba za ta zama 'yar siyasa ba har ma ta jagoranci gwamnatin Jamus muddin tsohuwar Jamus ta Gabas da ta Yamma ba su hade ba, kana kuma hakan ba zai taba faruwa ba da a ce kasar ta Hangari ba ta taka muhimmiyar rawa ba. 

An gudanar da bukuwan ne a cikin wani fata na samun ci gaban hadin kan kasashen nahiyar Turai maimakon rarrabuwar kawuna.