Ci gaban tanttanawa a game da rikicin nuklear Korea ta Arewa | Labarai | DW | 29.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban tanttanawa a game da rikicin nuklear Korea ta Arewa

Ƙasashen da ke shiga tsakanin rikicin nuklear Korea ta Arewa, ta ci gaba da tanttanawa a birnin Pekin na ƙasar Sin.

A yau asabar, su na gudanar da mahaurori agame da tallafin da ya cencenta su baiwa Pyong-Yang ta fannin makamashi ,a sakamakon alƙawarin da ta ɗauka na yin watsi da batun mallakar makaman nuklea.

A jiya juma´a,shugaban ƙasar Amurika Georges Bush, ya bayyana baiwa Korea ta Arewa taimakon dalla milions 25, kamin ƙarshen wannan shekara.

A cewar wakilin Amurika Kristopha Hill a tantanwar,akwai kyaukyawan alamu na kawo ƙarshen taƙƙadamar nulkear Korea ta Arewa nan bada jimawa.

Idan dai ba a manta ba , a watanin da su ka gabata, Korea ta Arewa ta rufe babbar tashar ta ta samar da makaman nuklea , ta kuma gayyaci hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea ta Majalisar Ɗinkin Dunia ta ziyarci ƙasar, don ganewa idon ta yadda hukumomi su ka cika alkawarin da su ka ɗauka.