1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ngozi Okonja-Iweala ta ziyarci Najeriya

March 15, 2021

A wani abun da ke zaman ziyararta ta farko, shugabar kungiyar Ciniki ta Duniya Ngozi Okonja-Iweala ta ce Najeriya na bukatar kara habaka kayayyakin da take sarrafawa domin samar da ayyuka tsakanin al'ummarta.

https://p.dw.com/p/3qfMu
Nigeria | Besuch WTO Generaldirektorin | Ngozi Okonjo-Iweala
Shugabar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala tare da shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Ubale Musa

Dakta Ngozi Okonja-Iweala dai na ziyararta ta farko a cikin kasar, tun bayan darewarta kan kujerar mai tasiri, a farkon wannan wata da muke ciki. To sai dai kuma ba ta boye bukatar neman sauyi ga yadda Tarayyar Najeriyar ke tafi da harkokin ciniki a tsakaninta da sauran kasashe na duniya ba. Bayan wata ganawa da shugaban kasar a Abuja dai, shugabar ta WTO ta ce akwai bukatar sauyi ga kasar da ke zaman babbar kasuwa a duniya amma kuma ba ta cin gajiyar ciniki tsakanin ta da saura kasashe a duniya.

Karin Bayani: Ngozi Okonjo-Iweala ta zama shugabar WTO

Ya zuwa yanzu dai a fada ta Okonjo-Iweala ciniki a tsakanin Najeriyar da ragowar kasashen duniya bai wuce kasa da kaso daya a cikin 100 ba da kuma mafi yawansa ke zaman na harkar man fetur, harkar kuma da ta fara zama tsohon yayi a duniya: "A kwai dama babba ga Najeriya ta kyautata matsayinta game da ciniki. A yanzu, cinikinmu da duniya bai wuce kaso  0.3 ba, a yayin kuma da cinikimu da kasashen Afirka ke zaman kaso 19  cikin 100, kana muna matsayi na 103 a cikin kasashe 167 ga bukatu na yau da na gobe."

Ngozi Okonjo-Iweala | neue WTO-Chefin
Shugabar kungiyar Ciniki ta Duniya wato WTO Ngozi Okonjo-IwealaHoto: Gian Ehrenzeller/KEYSTONE/dpa/picture alliance

A cewarta, wannan na nuni da cewar akwai bukatar mikewa a tsaye, domin inganta matsayin kasar da tattalin arzikinta ta hanyar ciniki: "Ni da shugaban kasa mun tattauna batun noma, yadda za mu kara wa kayan gonarmu daraja. Kamar yadda kuka sani, duniya na fuskantar sauyi daga mai ya zuwa makamashi mara illa ga muhalli. Kuma ya kamata mu fara wannan sauyi a kashin kanmu. Tabbas za mu bukaci man fetur da iskar gas dinmu na wasu shekaru da ke tafe, amma dai muna bukatar fara matsa wa zuwa makamashi mara illa. Dole ne mu kara sarrafa kayayyaki. Dole ne mu fara tunanin daga darajar kayanmu. Mai yasa hakan ke da muhimmanci? Saboda mu kara samar wa da al'ummarmu aiki, sannan kuma mu kara yin ciniki."

Karin Bayani: Najeriya na samun goyon bayan Amirka a WTO

Ana dai kallon rashin aikin yin na da ruwa da tsaki da karuwar talauci da ma aikata manyan laifukan da ya mamaye kasar a halin yanzu. Tuni dai kasar ta ce ta fara ganin haske daga shugabancin na Okonjo-Iweala da a cewar karamar ministar ciniki ta kasar Maryam Yalwaji Katagun ya kai ga karuwar bukatar man kade da ridi daga kasashen waje. To sai dai kuma in har Najeriyar tana shirin ganin daban a wannan lokaci, daga dukkan alamu bukatar kasashe na duniyar na samun damar cire iko na mallaki da ma samun allurar rigakafin annobar COVID-19, bai samu amincewa ta hukumar ba.

Südafrika I Coronavirus I Impfung
Wasu al'ummar Afirka sun fara karbar allurar riga-kafin coronavirusHoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

Okonjo-Iweala da a baya ta shugabanci kawancen riga-kafi ta duniya Gavi Alliance, ta ce ana bukatar share shekaru akalla hudu zuwa biyar kafin iya gina sababban cibiyoyin samar da rigakafin da kasashe na duniya ke da bukata yanzu. "Abun da nake roko shi ne mu kalli hanya ta uku, ita ce muna tafiya muna kuma taunar cingam. A yanzu in muka yafe ikon hada allurar, to ba za mu iya samar da allura ko daya ba. Na shafe shekaru biyar zuwa shida a cikin masana'antar riga-kafi, saboda na shugabanci kawancen Gavi. Muna bukatar akalla shekaru hudu zuwa biyar kafin iya kafa masana'antar yin allurar, saboda wahalar abun. Abun da nake cewa shi ne, mu kara yawan allurar da muke samarwa yanzu. Ga kasashen da ke tasowa wadanda ke da karfin hada allura kamar yadda India ke yi, suna samar da yawan allurar da ya kai biliyan guda a cibiyar Serem, mai yasa ba za mu yi haka ba?"

Karin Bayani:Najeriya da takarar Ngozi Oknojo-Iweala

Tarayyar Najeriyar dai na fatan sababbin dabarun sake ginin abubuwan more rayuwa irin kamar layin dogo da kara habaka karfin wutar lantarki, na iya taimaka mata kara yawan cinikin a sabuwar kasuwar kasashen nahiyar Afirka da ma tsakaninta da ragowar kasashen duniya.