1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace ta farko a matsayin shugabar WTO?

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 28, 2020

Manyan wakilan kungiyar Kasuwanci ta Duniya WTO, sun zabi Ngozi Okonjo-Iweala 'yar asalin Najeriya a matsayin mace ta farko da za ta jagoranci kungiyar.

https://p.dw.com/p/3kZMm
Ehemalige Außen- und Finanzminister Ngozi Okonjo-Iweala
Hoto: Fabrice Coffrini/AFP

Tun da farko kakakin kungiyar ta WTO Keith Rockwell ya shaidawa manema labarai cewa, bayan da wakilai daga manyan rassan kungiyar uku na duniya suka kwashe watanni hudu suna tattaunawa da kasashe mambobinta, akwai yiwuwar su yanke shawarar zabar Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugaba.

Karin Bayani: WTO: 'Yan Afirka uku na neman shugabanci

Wakilai 26 cikin 27 ne dai suka bayyana amincerwasu da Okonjo-Iwela. Amirka ce kasa daya tilo da ta ki goyon bayan zabar Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar kungiyar ba, inda ta goyi bayan ministar kasuwancin Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee.

Karin Bayani: Taƙaddama kan kasafin kuɗin tarayyar Najeriya

Sai dai Za a tabbatar mata da kujerar ne, bayan kasashe mambobin kungiyar 164 sun yanke hukunci a babban taronta na ranar tara ga watan Nuwamba mai zuwa. Mai shekar 66 a duniya, Okonjo-Iweala ta kasance mace ta farko da ta zama ministar kudi da kuma ministar harkokin kasashen waje a kasarta Najeriya, kuma tana da kwarewar aiki ta tsawon shekaru.