1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ngozi Okonjo-Iweala za jagoranci WTO

Uwais Abubakar Idris AH
February 8, 2021

A Najeriya samun goyon bayan da gwamnatin Amirka ta yi ga ‘yar takarar neman zama shugabar kungiyar cinikaiyya ta duniya, WTO,  bayan daukar watani ana tirka-tirka a kan lamarin ya sanya mayar da martani.

https://p.dw.com/p/3p3sL
Ehemalige Außen- und Finanzminister Ngozi Okonjo-Iweala
Hoto: Fabrice Coffrini/AFP

Wannan mataki da gwamnatin Kasar Amirkan ta dauka a karkashin shugaban kasar Joe Biden na fitowa karara a fili ya nuna goyon bayan kasar ga ‘yar takarar ta Najeriya Dr Ngozi Okonjo -Iweala ya share fage na kai wa ga wannan mukami ga ‘yar Najeriyar na zama shugabar kungiyar cinikaiyya ta duniya. Iat ce dai mace kuma bakar fata ta farko da za ta rike shugabancin wannan kungiya. Ja in ja da ma nuna isa da Amirkan ta yi a fafatawar kai wa ga wannan mataki musamman tsohon shugaban Kasar Donald Trump ya sanya jan hankalin jama’a zuwa ga wannan kungiya ta cinikaiyya ta duniya, tare da  tambayar muhimmancin da take da shi. Dr  Dr Ngozi Okonjo-Iweala dai ta rike mukamai masu yawa  a Najeriyar da kasashen duniya musamman zamanta babbar darakta hukumar bada lamuni  abin da ya sanyata zama wacce ta cancanata ta rike wannan mukami. bBakar fatar duniya na cike da fata ga jagorancin da za ta yi a wannan kungiya abin da ya sanya kalo komawa sama don ganin  salon jagorancinta da ke cike da kalubale.