1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shirin allurar rigakafin COVAX ya dauki hankula

Zainab Mohammed Abubakar RGB
February 26, 2021

Shirin samar da rigakafin corona a Afirka da rikicin kasar Somaliya sun dauki hankulan jaridun Jamus. An soma gudanar da shirin COVAX daga kasar Ghana da ke yankin yammancin Afirka.

https://p.dw.com/p/3pylf
Symbolbild Deutschland Medien
Hoto: imago/Ralph Peters

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta labari mai taken " An fara kai alluran COVAX zuwa Afirka". Jaridar ta ci gaba da cewar Ghana ta kasance kasa ta farko da ta karbi allurar rigakafin cutar corona a karkashin shirin samarwa kasashen Afirka matalauta wannan allura da duniya ke rubibin nemanta. Tuni dai rukunin farko na allurar ta COVAX ya isa birnin Accra fadar gwamnatin Ghana. Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya watau WHO da Hukumar Kula da Asusun yara ta UNICEF sun yi albishir din cewar, an kaddamar da wannan gagarumin shiri mai cike da tarihi na yin allurar rigakafi mafi girma, wanda za a fadada shi zuwa wasu gomman kasashe.

Ghana da ke yankin yammacin Afirka dai na zama kasa ta farko da ta ci gajiyar wannan shiri na tallafi ga kasashe matalauta da marasa galihu domin yaki da annobar corona ta Majalisar Dinkin Duniya, inda ta karbi allurar kamfanin Astra Zeneca guda dubu dari shida. A karkashin wannan shirin na COVAX, ana sa ran rarraba alluran rigakafin corona wajen miliyan dari uku da talatin ga kasashe kimanin dari da arba'in da biyar, kafin karshen wannan shekarar da muke ciki. A Afirka alal misali, ana saran yi wa kashi 20 daga cikin 100 na al'ummar nahiyar. Sai dai kwararru na ganin cewar wannan shirin tallafin allura ba zai magance matsalar gibin rarraba ta ba. 

Tanzanias Präsident John Pome Magufuli und Maalim Seif Shariff Hamad begrüßen sich mit Füßen
Shugaba Magufuli bai yarda akwai corona baHoto: Tanzania Presidential Office

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel karkata ta yi zuwa kasar Tanzaniya da labarinta mai taken " Addu'a maganin corona". Ta ce, Tanzaniya ba ta yi odar allurar rigakafi ba, saboda shugaban kasar na ganin cewar babu bukatar hakan. A daidai lokacin da duniya baki daya ke dakon karbar alllurar rigakafin, Tanzaniya ta juya wa abun baya. A kwanakin baya bayannan ne dai Shugaba John Magufuli, ya baiyana cewar, babu wannan cutar a tsakanin al'ummarsa. A cewarsa, adduo'in kwanaki uku da ya jagoranci al'ummar kasar miliyan sittin, ya fatattaki cutar daga wannan kasa ta yankin gabashin Afirka.

Ghana | AstraZeneca | COVAX-Impfstoff
Shirin samar da allurar rigakafin COVAXHoto: Francis Kororoko/REUTERS

A yanzu haka dai shugabannin kasashen Afirka na kuka da cewar, kasashen yammaci na Turai masu arziki su ne za su ci moriyar allurar da ake sarrafawa a wannan nahiyar. Akwai yiwuwar jiran shekaru a bangaren al'ummar Afrika da yawansu ya kai biliyan daya da digo uku, kafin allurar ta kai garesu. Sai dai a cewar shugaban na Tanzaniya wannan ba matsala ba ce, kasancewar allurar ba ta da wani tasiri. Magufuli ya na ganin cewar, idan da bature zai iya samar da allura cikin gaggawa haka, da ya samar da magungunan cutar AIDS da tarin fuka da zazzabin cizon sauro. Da yawan mutane dari uku da ke da corona a Tanzaniyar na a matsayin kasa ta 194 da ke fama da annobar. Daga batun COVID 19 sai kuma batun siyasa da tashe tashen hankula a Somaliya. Jaridar Die Tageszeitung ta yi sharhi mai taken " Babu kasa amma rigingimu sun mamaye ko'ina". 

Somalia Selbstmord-Bombe in Mogadischu
Somaliya na fama da rikici a gabanin zabeHoto: Farah Abdi Warsameh/AP Photo/picture alliance

Jaridar ta ci gaba da cewar, a wannan watan na Febrairu ne ya kamata a gudanar da zaben kasa baki daya a Somaliya. Sai dai bisa dukkan alamu an koma gidan jiya. Mutane biyar ne dai suka rasa rayukansu, a yayin da jami'an tsaro suka yi ta musayar wuta tsakaninsu. Musayar wuta a lokacin zanga-zanga a birnin Mogadishu a ranar Juma'ar da ta gabata, ya tabbatar da cewar har yanzu Somaliyar na cikin wadi na tsaka mai wuya tun bayan da aka tsayar da ranar 8 ga watan Febrairu a matsayin ranar zaben kasa baki daya da ya dace ya zama mai cikakken tarihi a siyasan wannan kasa.