1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yar Afirka ta farko shugabar WTO

Uwais Abubakar Idris LMJ
February 15, 2021

Bayan da Amirka ta bayyana goyon bayanta ga takarar Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a shugabancin kungiyar Ciniki ta Duniya, 'yar Najeriyar ta samu wannan matsayi.

https://p.dw.com/p/3pOlX
Nigeria Finanzminister Ngozi Okonjo-Iweala
Ngozi Okonjo-Iweala: Mace ta farko 'yar Afirka shugabar kungiyar Ciniki ta DuniyaHoto: NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images

Bayan daukar watanni ana tirka-tirka a kan takarar shugabancin kungiyar Cinikin ta Duniya WTO da 'yar Najeriyar da ke zaman 'yar Afirka ta farko da ta kai ga wannan matsayi, a karshe Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta yi nasarar samun darewa kan wannan mukami. Wannan batu dai ya sanya 'yan kasarta wato Najeriya mayar da martani da kuma yin nazari kan muhimmancin da wannan matsayi ke da shi ga kasar a fannoni da dama.

Karin Bayani: Ngozi Okonjo-Iweala za ta zama shugabar WTO

Matakin gwamnatin kasar Amirkan karkashin sabon shugaban kasar Joe Biden na fitowa karara wajen nuna goyon bayan kasar ga 'yar takarar ta Najeriya Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ya share fage gare ta na kai wa ga wannan mukami na shugabancin kungiyar Cinikayya ta Duniya.
Ja-in-ja da ma nuna isa da Amirkan ta yi a fafatawar kai wa ga wannan mataki musamman tsohon shugaban kasar Donald Trump ya sanya jan hankalin 'yan Najeriya zuwa ga kungiyar Cinikaiyyar ta Duniya, tare da tambayar muhimmancin da take da shi da har aka yi ta zaryar kai wa ga jagorantar ta. Dakta Ngozi Okonjo-Iweala dai ta rike mukamai masu yawa a Najeriyar da kasashen duniya, musamman zamanta babbar darakta a Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya, abin da ya sanya ta zama wacce ta cancanta ta rike wannan mukami.

BG Kandidaten für WTO-Spitzenjob - Die acht Kandidaten
Ngozi Okonjo-Iweala ce ta samu nasara cikin 'yan takara takwas, bayan da suka janyeHoto: picture-alliance/dpa/KEYSTONE/S. Di Nolfi

Karin Bayani: 'Yan Afirka uku na neman shugabancin WTO

'Yan Najeriyar dai kamar Amara Nwakpa Daraktan dubarun tsare-tsare na Gidauniyar 'Yar'adua da ke Abuja, ya bayyana murnarsa: "Na yi matukar farin ciki da naji cewa Ngozi Okonjo-Iweala za ta zama shugabar kungiyar Cinikayya ta Duniya, mace bakar fata ta farko za ta shiga kundin tarihi na zama shugabar wannan kungiya, wannan abin alfahari da farin ciki ne a gareni a matsayina na dan Najeriya mai goyon bayanta."