1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama kan kasafin kuɗin tarayyar Najeriya

August 2, 2012

An tashi baran baran a wata ganawa tsakanin ministar kuɗin Najeriya Okonjo-Iweala da kuma 'yan majalisar dattawan ƙasar kan kasafin kuɗin ƙasar na bana.

https://p.dw.com/p/15ino
Ngozi Okonjo-Iweala, coordinating minister for economy and finance of Nigeria, speaks during a plenary session at the 42nd annual meeting of the World Economic Forum, WEF, in Davos, Switzerland, Thursday, Jan. 26, 2012. The overarching theme of the meeting, which will take place from Jan. 25 to 29, is "The Great Transformation: Shaping New Models". (AP Photo/Keystone, Jean-Christophe Bott)
Hoto: dapd

A wani abun dake zaman gaza kaiwa ga warware taƙaddamar dake tsakanin majalisun tarrayar Najeriya biyu da kuma ɓangaren zartarwar ƙasar an kammala wata ganawa baran baran tsakanin ministar kuɗin ƙasar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala da kuma 'yan majalisar dattawan ƙasar.

Tun ba a kai ko-ina ba dai taƙaddama ta fara ɓarkewa a tsakanin ministar kuɗin da bayan share tsawon lokaci tana wasan ɓuya da kuma 'ya'yan majlisar dattawan Najeriyar dake neman ta ruwa a jallo domin neman ba'asin gaza aiwatar da kasafin kuɗin ƙasar na bana.

Ta dai share tsawon kusan awoyi huɗu tana ƙoƙarin sauya tunanin 'yan majalisar ta kuma kai ga amsa jerin tambayoyin ya aka yi aka haife ka ga ministar da ake yiwa kirari da kafi mataimakin shugaban ƙasa da kuma majalisar ke zargi da ƙoƙarin ruɗa ƙasar kan kasafin na bana da ke ci-gaba da jawo taƙaddama a tsakanin ɓangarorin gwamnatin ƙasar biyu.

Gaza aiiwatar da kasafin kudi

Ministar dai ta ce ta ji ta gani ta kuma shaida cewar gwamnatin ƙasar ba ta da laifi ga ƙoƙarin aiwatar da kasafin da a cewar ta ke tafiya bisa ƙa'ida kuma ya kama hanyar tasiri ga makomar ƙasar ta Najeriya.

Torbogen am Stadtrand der nigerianischen Hauptstadt Abuja, aufgenommen am Donnerstag (02.08.2007). Foto: Gero Breloer dpa +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

"Mun fara aiwatar da kasafin kuɗin nan a watan Afrilu wato wata huɗu da suka wuce, kuma ya zuwa yanzu da ya kamata mu saki Naira miliyan dubu 446, yanzu mun saki milliyan dubu 404, kaɗan ya gaza daga cikin wannan adadi. An yi amfani da Naira miliyan dubu 184 abun da aka yi kasafi kenan, abun da ya kamata mu saki kenan a duk wata ba mu riƙe wata dukiya ba."

Bayanan ministar ba su gamsar da 'yan majalisa ba

To sai dai kuma riƙe dukiyar ƙasa ko kuma ƙoƙarin cika ƙa'idar kasafi, daga dukkan alamu matsayin ministar ya gaza kaiwa ga burge 'yan majalisar da suka ce ba su gamsu da jerin bayanan da a cikin su ministar ta ce kasafin kuɗin ƙasar na tafiya dai dai ba.

Senator Ahmed Lawal dai na zaman ɗan majalisar dattawan Najeriyar daga jihar Yobe.

Ƙoƙarin daɗi a baka ko kuma ƙoƙarin kaucewa fushin yan majalisa dai , a baya dai tarrayar kasar ta Nigeria ta sha fama da matsalar gaza kaiwa ga aiwatar da kasafin ba tare da tada hankali a ɓangaren 'ya'yan majalisar ba.

A photograph made available 19 August 2010 shows the Chevron oil facility under contruction in Escravos, 56 miles from Warri in the oil rich Niger delta region of Nigeria 17 August 2010. Nigeria is the fifth largest exporter of oil to the United States and the largest producer of oil in Africa. For decades, thousands of spills across the fragile Niger Delta have hampered the livelihoods of fishermen and farmers, contaminated water sources and polluted the ground and air. Approximately 300 spills are estimated each year. Some are small and some are continuous leaks but compounded they continue to pollute the delta. EPA/GEORGE ESIRI Schlagworte Fabrik, Erdöl, düster, Ufer, Wolken, Schiff, dunkel, Öl, Wirtschaft, Himmel, Schiffe, Natur, Industrie, Verkehr, Unternehmen, Gewässer
Najeriya ta dogara ga man fetir don samun kuɗaɗen shigaHoto: picture-alliance/dpa

To sai dai kuma a bana sun kai ga mancewa da banbanaci bangaranci dama jamiyyar da ta kawo su dandalin majalisar wajen tunkarar batun da kuma a cewar senator Abdul Ningi dake zaman mataimakin shugaban masu rinjayen majalisar ke da ruwa da tsaki da halin da ƙasar ke ciki a yanzu.

Ana dai cigasba da ta'allaka shi kansa batun rashin tsaron dake ƙara ta'azzara cikin ƙasar da muguwar fatarar da ta yi aure tana shirin tarewa a tsakanin al'ummar ƙasar ta Najeriya a yanzu haka.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal