1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari da Atiku na neman hanyoyin nasara a 2019

Uwais Abubakar Idris
October 8, 2018

Fitar da 'yan takarar neman shugaban kasa da manyan jam'iyyu biyu na PDP da APC suka yi a Najeriya ya nuna fafatawar da za’a yi a 2019, abin da ka iya sauya yakin neman zabe a kokuwar kaiwa ga samun shugabancin kasar.

https://p.dw.com/p/36Ao4

Nasarar da tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ta ‘yan adawa ya samu, bayan da ya kayar da mutane 11 da suka yi takara, ya nuna cewar shi ne ke kalubalantar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulki. Wannan ya bude sabon babi a guguwar siyasar da ke kadawa, domin kar-ta- san- kar a tsakanin mutanen guda biyu.

Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja ya bayyana hasashensa ga irin fafatawar da za'a yi, inda ya ce " Za'a yi fafatawa mai zafin gaske ganin cewar Atiku Abubakar hamshakin dan siyasa ne da kuma wanda yake yi wa adawa shugaban kasa da ke rike da madafun iko.