Bude makarantu a Liberiya mai fama da Ebola | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 20.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Bude makarantu a Liberiya mai fama da Ebola

Sake bude makarantu a Liberiya da yakin da ake yi da Boko Haram da kuma rayukan 'yan Afirka da ke salwanta a tekun Bahar Rum.

Labaran Afirka da suka fi daukar hankalin jaridun na Jamus a wannan mako sun hada da sake bude makarantu a Liberiya mai fama da cutar Ebola da yakin da ake yi da Boko Haram sai kuma rayukan 'yan Afirka da ke salwanta a tekun Bahar Rum.

A sharhin da ta rubuta game da komawar yara makaranta a kasar Liberiya jaridar Neue Zürcher Zeitung kyakkyawan fata ta yi wa kasar mai fama da matsalar cutar Ebola.

A ranar Litinin 'yan makaranta sun koma daukar darasi a Liberiya bayan jinkiri na tsawon watanni biyar sakamakon mummunar annobar cutar Ebola da kasar da ke yammacin Afirka ta yi fama da ita a tsakiyar shekarar 2014. Jaridar ta ce in banda kewayen da suka saba da shi komai ya zama sabo ga yaran musamman 'yan shekarar karatu na farko.

Hada karfi wajen yakar 'yan tarzoma

Boko Haram haramun inji jaridar Die Tageszeitung tana mai nuni da yakin da ake yi da kungiyar ta masu tsattsauran ra'ayi.

Ta ce sojoji sun yi ikirarin samun gagarumar nasara a kan mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya amma a lokaci daya sun bude wuta kan wasu matasa da suka halarci wani gangamin siyasa na madugun adawa Muhammad Buhari a garin Maiduguri na jihar Borno bayan wata takaddama da suka yi da sojojin wadanda aka tura su kare Buhari. Hakan ta faru ne lokacin da matasan suka tsare motoci dauke da albarusan da sojojin suka shiga da su garin ta jirgin sama kuma suka bi da su tsakiyar gari. A kuma can filin daga rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na kasa da na sama sun sake kwace wasu yankuna daga hannun mayakan na Boko Haram a cikin wannan mako. A daidai wannan lokaci gwamnatin Nijar ta kira wata zanga-zanga ta kasa baki daya karkashin taken Boko Haram haramun, don nuna adawa da aikace-aikacen kungiyar da suka saba wa koyarwar addinin musulunci.

Gara kasadar bi ta teku a shigo Turai da zama a Afirka

Matsalar bakin haure musamman 'yan Afirka da ke daukar kasadar bi ta tekun Bahar Rum suna shigowa Turai, ta dauki hankalin jaridar Neue Zürcher Zeitung.

Ta ce 'yan gudun hijirar sun san irin hatsarin da ke cikin wannan tafiya amma duk da haka suna daukar wannan kasada. A wannan shekara tun a cikin lokacin sanyin hunturu dubun dubatan bakin haure suka yi yunkurin yin wannan tafiya a tekun Bahar Rum don shigowa Turai. Ko da yake an samu asarar rayukan wasu daruruwa a cikin tekun, amma duk da haka a kullum ana samun masu daukar wannan kasada. Dalili dai shi ne 'yan Afirka sun fi ba da muhimmanci ga amfanin da za su samu idan suka yi nasarar shigowa Turan, fiye da rayukansu.

Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuya

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan makon ta leka kasar Afika ta Kudu ne inda ta ce:

Yanzu haka shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma yana cikin matsin lamba. Baya ga zargin cin hanci da rashawa, yana kuma fuskantar babban kalubale na cikin gida wato batun filaye. Shekaru 20 bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata, har yanzu akasarin gonakin kasar suna hannun tsiraru fararen fata. Saboda haka yanzu shugaba Zuma ya sanar da kafa wata sabuwar doka da za ta takaita wa baki 'yancin sayen filaye, sannan su kuma 'yan kasa za a rage girmar filin da za su iya mallaka. Sai dai tun yanzu wannan mataki na shan suka musamman daga manyan manoma na kasar.