Bahar Rum na zama tekun da ya raba kasashen Afirka da Turai, wanda ya yi iyaka da kasashen yankin arewacin Afirka da kuma wani bangaren Turai.
A cikin shekarun da suka gabata masu safarar mutane daga arewacin Afirka suna amfani da tekun wajen shigar da mutane daga Afirka zuwa Turai ta barauniyar hanya, kuma saboda rashin ingancin jiragen ruwa gami da wasu matsaloli mutane da dama suna hallaka a kan hanyar.