1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An gano gawarwakin bakin haure 10 a cikin teku

Ramatu Garba Baba
April 12, 2023

Bakin haure kimanin goma aka gano gawarwakinsu a cikin tekun Tunisiya, duk sun fito ne daga kasashen yankin Kudu da hamadar Sahara da zummar shiga Turai.

https://p.dw.com/p/4PxgQ
Karuwar nutsewar jiragen bakin haure a cikin teku
Karuwar nutsewar jiragen bakin haure a cikin tekuHoto: Ryan Remiorz/Canadian Press/AP/picture alliance

Wasu bakin haure kimanin goma da suka fito daga kasashen Kudu da hamadar Sahara sun mutu bayan da jirgin ruwansu ya nutse a tekun ruwan Tunisiya, jirgin na kan hanyarsa ta zuwa mashigin ruwan Italiya a lokacin da nutse. Majalisar Dinkin Duniya a na ta bangaren, ta ce, watan Janairu zuwa Maris na wannan shekarar ta 2023, sun kasance watanni mafi muni da aka samu karuwar kwararan bakin haure da kuma mutuwarsu a cikin teku, bakin haure kimanin dari hudu da arba'in da daya aka tabbatar sun rasa rayukansu a yayin yunkurin shiga Turai ta barauniyar hanya da zummar nemawa kansu rayuwa mai inganci in ji majalisar.